2 Kings 5:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ يَكَرَنْتَ وَسِيڧَرْ، سَيْ يَيَيَّاغٜىٰ رِيغُنَنْسَ دُوانْ بَڧِنْ ثِكِ يَثٜىٰ «نِے اللَّهْ نٜىٰ، مَيْ عِيَ كَشٜىٰ كُواْ مَيْ عِيَ بَادَ رَيْ؟ دُوانْمٜىٰ سَرْكِنْ سُورِيَ ذَيْ عَيْكُواْ دَ سَڧُواْ ثٜىٰوَ إِنْ وَرْكَرْدَ مُتُمْ دَغَ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِنْسَ؟ دُوبِے يَدَّ مُتُمِنَّنْ يَكٜىٰ نٜىٰمَنَ دَ ڢَطَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”