2 Kings 7:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ɗaya daga cikin fadawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birni, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu ne. Bari mu aika, mu gani.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَيَ دَغَ ثِكِنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِنْ يَثٜىٰ «مُعَيْكَ مُتَنٜىٰ سُطَوْكِ دَوَكِ بِيَرْ وَطَنْدَ سُكَ رَغُ، سُتَڢِے سُدُوبِے أَبِنْدَ مُكَجِ؞ غَمَا عِدَنْ وَنِ أَبُ يَڢَرُ دَسُو، بَذَيْ ذَمَ بَبَّرْ هَسَرَبَ ڢِيٜىٰدَ عِدَنْ سُنْ ذَوْنَ تَرٜىٰدَمُو عَبِرْنِنْ، سَبُواْدَ دُكَنْمُ ذَمَنْ مُتُوَانٜىٰ مُكٜىٰ عَثِكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ɗaya daga cikin fādawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birnin, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra'ilawan da suka riga suka mutu. Bari mu aika, mu gani.”