2 Kings 7:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan jama’a suka fita suka kwashi ganima a sansanin Arameyawa. Aka kuwa sayar da gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel guda, yadda Ubangiji ya faɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنْ سَمَرِيَ سُكَ ڢِتَ أَغُجٜىٰ سُكَ تَڢِے سَنْسَنِنْ يَاڧِنْ سُرِيَاوَا سُكَ ݣُوشِ كَايَ؞ سَيْ عَكَ سَيَرْ دَ مُودُ طَيَ نَغَارِنْ حَڟِ عَكَنْ أَظُرْڢَا غُدَا، سَعَنً مُودُ بِيُ نَهَڟِنْ بَلٜىٰ عَكَنْ أَظُرْڢَا غُدَا، بِسَغَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan mutane suka fita, suka washe sansanin Suriyawa. Aka kuwa sayar da mudu na lallausan gari da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel ɗaya ɗaya kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa.