2 Kings 7:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haka kuwa ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya ce wa sarki, “Gobe war haka, za a sayar da mudun gari shekel guda, mudun sha’ir biyu ma a shekel guda, a ƙofar Samariya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَكُوَ كَسَنْثٜىٰ كَمَرْ يَدَّ مُتُمِنْ اللَّهْ يَڢَطَا وَسَرْكِے ثٜىٰوَ كَاڢِنْ وَرْهَكَ غُواْبٜىٰ، ذَاعَ سَيَرْ دَ مُودُ بِيُ نَهَڟِنْ بَلٜىٰ عَكَنْ أَظُرْڢَا غُدَا، حَكَمَا مُودُ طَيَ نَغَارِنْ حَڟِ عَكَنْ أَظُرْڢَا غُدَا عَڧُواْڢَرْ بِرْنِنْ سَمَرِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya faru daidai yadda annabi Elisha ya ce wa sarki, “Za a sayar da mudu biyu na sha'ir, da mudu na lallausan gari a bakin shekel ɗaya ɗaya gobe war haka a ƙofar birnin Samariya.”