2 Kings 7:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai wani hafsa mataimakin sarki ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Sai Elisha ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ وَنْدَ سَرْكِے يَكٜىٰ دُواْغَضَ عَكَنْسَ يَثٜىٰ وَمُتُمِنْ اللَّهْ «كُواْ دَ يَهْوٜىٰهْ دَ كَنْسَ ذَيْبُوطٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْ سَمَ، وَنَّنْ أَبُ بَذَيْ عِيَ ڢَرُوَ بَ سَمْ!» أَلْيَسَعَ كُوَ يَثٜىٰ مَسَ «ذَاكَ غَنِ دَ عِدَنُونْكَ، عَمَّا بَذَاكَثِبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”