2 Kings 7:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da kutaren nan suka kai bakin sansanin, sai suka shiga wani tenti, suka ci, suka sha, suka kwashi azurfa, da zinariya, da riguna, suka tafi, suka ɓoye su. Sa’an nan suka koma, suka shiga wani tenti, sai suka kwashi kaya daga ciki, suka kuma ɓoye su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ مَاسُ ثُوتَرْ ڢَتَرْ نَنْ حُطُ سُكَ كَيْ بَاكِنْ سَنْسَنِنْ، سَيْ سُكَ شِغَ وَنِ تٜىٰنْتِ سُكَثِ سُكَشَا، سُكَ ݣُوشِ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ دَ رِيغُنَ، سُكَ تَڢِے سُكَ ٻُواْيٜىٰسُ؞ سَعَنً سُكَ كُواْمَ سُكَ شِغَ وَنِ تٜىٰنْتِ، سَيْ سُكَ ݣُوشِ كَايَ دَغَ ثِكِ، سُكَ كُمَ ٻُواْيٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kutaren nan suka zo sansanin, sai suka shiga wata alfarwa, suka ci suka sha. Suka kwashe azurfa, da zinariya, da tufafi, suka tafi suka ɓoye. Suka koma suka shiga wata alfarwa kuma, suka kwashe abubuwan da suke cikinta. Suka tafi suka ɓoye su.