2 Kings 8:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هَظَيٜىٰلْ يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، دُوانْمٜىٰ كَكٜىٰ كُوكَا؟» أَلْيَسَعَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «سَبُواْدَ نَسَنْ مُغُنْتَارْ دَ ذَاكَيِ وَمُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَاكَ ڧُواْڧُّواْنٜىٰ كَتَنْغَرْ بِرَنٜىٰنْسُ، ذَاكَ كَكَّشٜىٰ سَمَارِنْسُ دَ تَكُواْبِے، ذَاكَ ڢَرْڢَشٜىٰ كَوُنَنْ يَارَنْسُ ڧَنَانَا عَڧَسَا، ذَاكَ يَيَّاغٜىٰ ثِكِنْ مَاتَا مَاسُ جُونَ بِيُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”