2 Kings 8:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا وَشٜىٰغَرِ سَيْ هَظَيٜىٰلْ يَطَوْكِ بَرْغُواْ يَجِڧَ أَ ضُوَ يَرُڢٜىٰ ڢُسْكَرْ سَرْكِے، حَرْ سَيْ دَ يَمُتُ؞ تَهَكَ هَظَيٜىٰلْ يَهَوْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ بٜىٰنْهَدَدْ؞ ﴿شٜىٰكَرَا 848-841 كَاڢِنْ حَيْڢُوَرْ عِيسَىٰ ﴾
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa'an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu. Sai ya hau gadon sarautarsa.