2 Kings 8:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يُواْرَمْ يَكُواْمَ بِرْنِنْ يٜىٰظِرٜىٰيٜىٰلْ دُواْمِنْ عَيِ مَسَ جِنْيَرْ رَوْنُكَنْ دَ سُرِيَاوَا سُكَيِ مَسَ أَ رَمُواتْ؞ سَيْ سَرْكِے أَهَظِيَ طَنْ يٜىٰهُواْرَمْ نَ يَهُودَ يَغَنْغَرَ دُواْمِنْ يَظِيَرْثٜىٰ شِ دَيَكٜىٰ يَنَ ثِيوُاْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki Yehoram ya koma zuwa Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da yake yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya, ɗan Yoram, Sarkin Yahuza ya tafi ya ziyarci Yehoram ɗan Ahab cikin Yezreyel saboda yana ciwo.