2 Kings 8:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَكٜىٰ ڢَطَا وَسَرْكِے عَكَنْ يَدَّ أَلْيَسَعَ يَتَادَ مَتَتُّو، سَيْغَا مَثٜىٰنْ دَ أَلْيَسَعَ يَمَيْدَ رَنْ طَنْتَ تَشِغُواْ تَنَ كُوكَا غَ سَرْكِے يَسَا أَ مَيَرْ مَتَ دَ غِدَنْتَ دَ كُمَ غُواْنَرْتَ؞ سَيْ غٜىٰهَظِ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، يَا سَرْكِے، غَ مَثٜىٰنْ! غَا كُمَ طَنْتَ وَنْدَ أَلْيَسَعَ يَمَيْدَ رَنْسَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A sa'ad da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya ta da matacce, sai ga matar da ya ta da ɗanta daga matattu, ta zo ta roƙi sarki ya mayar mata da gidanta da gonarta. Sai Gehazi ya ce, “Ran sarki ya daɗe, ai, ga matar, ga kuma yaronta wanda Elisha ya tashe shi daga matattu.”