2 Kings 8:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْيَسَعَ يَتَڢِے دِمَشْڧُ لُواْكَثِنْ دَ سَرْكِے بٜىٰنْهَدَدْ نَ سُورِيَ يَنَ ثِكِنْ رَشِنْ لَاڢِيَ؞ سَيْ وَنِ يَڢَطَا وَ بٜىٰنْهَدَدْ ثٜىٰوَ أَلْيَسَعَ مُتُمِنْ اللَّهْ يَذُواْ حَرْ نَنْ غَرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan,