2 Kings 9:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ أَنَّبِے أَلْيَسَعَ يَكِرَا طَيَ دَغَ ثِكِنْ ڧُنْغِيَرْ أَنَّبَاوَا يَثٜىٰ مَسَ «يِشِرِ، كَطَوْرَ رِغَرْكَ دَ طَمَرَ، كَطَوْكِ ݣُولَبَرْ مَنْ ظَيْتُنْ أَ حَنُّنْكَ، كَتَڢِے رَمُواتْ تَڧَسَرْ غِلٜىٰيَدْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad.