2 Kings 9:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُو يَجَا بَكَنْسَ دَ دُكَنْ ڧَرْڢِنْسَ، يَسَكٜىٰ كِبِيَ، تَهَرْبِے يُواْرَمْ ڟَكَانِنْ كَڢَطَرْسَ حَرْ تَسُواْكِ ذُوثِيَارْسَ؞ سَيْ يُواْرَمْ يَڢَاطَ ثِكِنْ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa.