2 Kings 9:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَرْكِے أَهَظِيَ نَ يَهُودَ يَغَ حَكَ، سَيْ يَغُدُ يَبِے حَنْيَرْ بٜىٰتْ هَغَّنْ؞ يٜىٰهُو كُوَ يَبِے شِ يَيِ إِيهُ يَثٜىٰ «كُهَرْبٜىٰ شِ، شِے مَا!» سُكَ هَرْبٜىٰ شِ عَثِكِنْ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِنْسَ دَيْدَيْ يَنَ تَڢِيَ أَ هَوَنْ غُرْ، وَنْدَ يَكٜىٰ كُسَدَ إِبْلٜىٰيَمْ؞ سَيْ يَغُدُ ذُوَا مٜىٰغِدُّواْ يَمُتُ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan. Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.