2 Peter 1:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَوُرِنْ أَبُبُوَنَّنْ يَبَامُ مَنْيَنْ أَلْكَوَرَنْسَ مَاسُ دَرَجَ، دُواْمِنْ تَوُرِنْسُ، كُإِيَ تَرَيَّ دَشِ ثِكِنْ اللَّهْ نْتَكَرْسَ، كُكُمَ ڟِيرَا دَغَ مُغُنْتَارْ دَتَكٜىٰ عَدُونِيَا وَدَّ مُوغَيٜىٰنْ شَعَوَثٜىٰ شَعَوَثٜىٰ سُكٜىٰ جَٰوُاْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa.