2 Samuel 1:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَكَنْ يُواْنَتَنْ مَيْ كَشٜىٰوَ نٜىٰ، تَكُواْبِنْ طَالُوتَ مَرَرْ جِنْڧَيْ نٜىٰ؞ يَنَكَشٜىٰ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ، يَنَكَشٜىٰ أَبُواْكَنْ غَابَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bakan Jonatan mai kisa ne, Takobin Saul ba shi da jinƙai, Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.