2 Samuel 10:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سُواْجُواْجِنْ سُورِيَ سُكَ غُدُ دَغَ غَبَنْ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ دَاوُدَ دَ سُواْجُواْجِنْسَ سُكَ كَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ سُورِيَ مَاسُ هَوَنْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ طَرِے بَݣَويْ دَ كُمَ سُواْجُواْجِ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِ دُبُو أَرْبَعِنْ؞ سُكَ بُغِ شُواْبَكْ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْ سُورِيَ، حَرْ يَمُتُ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra'ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba'in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu.