2 Samuel 10:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ هَنُنْ يَكَامَ مَاسُ حِدِمَرْ نَنْ نَ دَاوُدَ؞ دُواْمِنْ يَوُلَڧَنْتَاسُ، سَيْ يَ أَسْكٜىٰ غٜىٰمُنْسُ تَغٜىٰڢٜىٰ طَيَ؞ يَكُمَ يَيَّنْكٜىٰ مُسُ رِيغُنَنْسُ أَدَيْدَيْ طُوَوُنْسُ؞ سَيْ يَسَلَّمٜىٰسُ سُتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa'an nan suka sallame su.