2 Samuel 11:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ شٜىٰكَرَا تَسَاكٜىٰ كٜىٰوَيُواْوَ، لُواْكَثِنْ دَ سَرَاكُنَ سُكَنْ ڢِتَ يَاڧِ، سَيْ دَاوُدَ يَعَيْكِ يُواْوَبْ دَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِنْسَ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ تَڢِے سُكَ هَلَّكَ أَمُّواْنَاوَا؞ سُكَ كُمَ كٜىٰوَيٜىٰ بِرْنِنْ رَبَّهْ؞ عَمَّا دَاوُدَ يَيِ ذَمَنْسَ أَ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra'ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.