2 Samuel 11:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da aka gaya wa Dawuda, “Uriya bai tafi gida ba,” sai Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Ba ka zo daga wuri mai nisa ba? Me ya sa ba ka je gida ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَرْكِے دَاوُدَ يَسَامِ لَابَرِ ثٜىٰوَ عُرِيَ بَيْ ݣُونَ أَغِدَنْسَبَ، سَيْ يَكِرَشِ يَثٜىٰ مَسَ «كَا ڢِتُواْ دَغَ تَڢِيَ مَيْ نِيسَ، دُوانْمٜىٰ بَكَتَڢِے غِدَنْكَبَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”