2 Samuel 11:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ƙara dakata a nan kwana ɗaya, gobe kuwa in sallame ka.” Saboda haka Uriya ya dakata a Urushalima a ranar, da kuma ta biye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَثٜىٰ وَ عُرِيَ «كَذَوْنَ دَنِے يَوْ؞ غُواْبٜىٰ كُوَ ذَنْسَا كَكُواْمَ وُرِنْ يَاڧِنْ؞» سَبُواْدَ حَكَ عُرِيَ يَذَوْنَ أَ عُرُوشَلِيمَ رَانَرْ نَنْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.