2 Samuel 11:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَكُ تُنَ دَ أَبِنْدَ يَڢَرُ دَ أَبِمٜىٰلٜىٰكْ طَنْ يٜىٰرُبّٜىٰشٜىٰتْ بَ؟ أَيْ، أَ تٜىٰبٜىٰظْ مَثٜىٰثٜىٰ تَجٜىٰڢَ دُوڟٜىٰنْ نِڧَ دَغَ كَنْ كَتَنْ‌غَرْ بِرْنِنْ، دُوڟٜىٰنْ كُوَ يَڢَاطَ مَسَ عَكَيْ، يَكَشٜىٰشِ نَنْ تَكٜىٰ؞ دُوانْمٜىٰ كُو كُمَ كُكَجٜىٰ كُرْكُسَدَ كَتَنْ‌غَرْ بِرْنِنْ؟› عِدَنْ سَرْكِے دَاوُدَ يَيِ تَمْبَيَ حَكَ، كَثٜىٰمَسَ، ‹مَيْ حِدِمَرْكَ عُرِيَ مُتُمِنْ هِتِّ شِے مَا يَمُتُ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba'al? Ba mace ce a Tebeze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”