2 Samuel 11:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَتُورَ یَنْ عَيْكَ سُكَٰوُاْتَ؞ دَتَذُواْ وُرِنْسَ، سَيْ يَݣُونَ دَ عِتَ؞ أَ لُواْكَثِنْ كُوَ تَغَمَ ڟَبْتَثٜىٰ كَنْتَ دَغَ جِنِنْ هَيْلَ؞ سَعَنً تَكُواْمَ غِدَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa'an nan ta koma gidanta.