2 Samuel 12:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً أَ رَانَ تَبَݣَويْ طَنْ يَمُتُ؞ مَاسُيِ وَ دَاوُدَ حِدِمَ سُكَجِڟُواْرُواْ سُڢَطَا مَسَ ثٜىٰوَ يَرُوانْ يَمُتُ؞ غَمَا سُنْيِ تُنَانِ ثٜىٰوَ «عِدَنْ حَرْ بَيْجِمُبَ سَعَدَّ يَرُوانْ يَكٜىٰدَ رَيْ، تَيَيَا ذَامُ ڢَطَا مَسَ ثٜىٰوَ يَرُوانْ يَمُتُ؟ أَيْ، ذَيْ عِيَيِ وَكَنْسَ ٻَرْنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”