2 Samuel 12:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ɗauke rawanin daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti, na zinariya, an kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, aka aza shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga garin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَسَا عَكَ ثِرٜىٰ هُولَرْ مُلْكِ دَغَ كَنْ سَرْكِنْسُ، عَكَسَا مَسَ عَكَيْ؞ نَوْيِنْ ظِينَارِيَ تَهُولَرْ سَرْكِنْ كُوَ يَكَيْ وَجٜىٰنْ كِلُواْ تَلَاتِنْ دَ بِيَرْ؞ هُولَرْ مُلْكِ كُمَ تَنَدَ أَدُوانْ دُوَڟُو مَاسُ دَرَجَ أَجِكِنْسَ؞ سَعَنً دَاوُدَ يَݣُوشِ كَايَنْدَ يَڨُوثٜىٰ عَيَاڧِ مَاسُيَوَ دَغَ ثِكِنْ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa'an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin.