2 Samuel 12:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً وَتَرَانَ سَيْ مَيْ أَرْزِڧِنْ يَيِ بَڧُواْ؞ عَمَّا بَيْ سُواْ يَطَوْكِ طَيَ دَغَ ثِكِنْ تُمَكِنْسَ كُواْ شَانُنْسَ يَشِرْيَ وَبَڧُوانْ عَبِنْثِبَ؞ أَمَيْمَكُوانْ حَكَ، سَيْ يَكَامَ یَرْ تُنْكِيَ طَيَ تَتَلَكَنَّنْ يَيَنْكَ وَبَڧُوانْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo 'yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”