2 Samuel 14:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.” Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَاسَاكٜىٰ ثٜىٰ مَسَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، إِنَ ضُواْڧُوانْكَ كَتُنَ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكَ؞ كَدَ كَبَرْ مَيْبِنْ حَكِّنْ جِنِنْ طَانَ يَڧَارَ كَٰوُاْ هَلَّكَ، دُواْمِنْ كَدَ طَانَ وَنْدَ يَرَغُ يَمُتُ؞» سَرْكِے دَاوُدَ يَثٜىٰ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ ثٜىٰوَ كُواْ غَاشِنْ كَنْسَ غُدَا طَيَ بَذَيْ ڢَاطِ ڧَسَابَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta ce, “Ina roƙonka, ya sarki, ka rantse da Ubangiji Allahnka, kada a bar masu bin hakkin jini su yi ramako, don kada su kashe ɗana.” Ya ce mata, “Na rantse miki da zatin Ubangiji, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba.”