2 Samuel 14:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?” Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَتَمْبَيٜىٰتَ يَثٜىٰ «أَݣَويْ حَنُّنْ يُواْوَبْ عَثِكِنْ وَنَّنْ ذَنْثٜىٰ نَاكِ كُواْ؟» سَيْ مَثٜىٰنْ تَأَمْسَ تَثٜىٰ «عِ، رَنْكَيَدَطٜىٰ، سَرْكِے، نَا ضَنْڟٜىٰ دَكَيْ، أَيْ، بَابُوَنْدَ ذَيْ عِيَ ثٜىٰوَ ‹أَعَ› غَا تَمْبَيَرْنَنْ دَكَيِ؞ يُواْوَبْ نٜىٰ يَعُمَرْثٜىٰنِ إِنْيِ حَكَ؞ شِينٜىٰ كُمَ يَڢَطَا مِنِ دُكَنْ أَبِنْدَ ذَنْثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?” Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.