2 Samuel 14:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma macen da ta fito daga Tekowa ta ce, “Ranka yă daɗe, sarki! Bari alhakin shari’arka yă kasance a kaina da gidan mahaifina, kai sarki da gidan mulkinka, ba ku da laifi a ciki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَثٜىٰنَّنْ دَغَ تٜىٰكُواْوَ تَڧَارَ دَ ثٜىٰوَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، سَرْكِے! بَرِ أَلْحَكِنْ شَرِيعَرْكَ يَكَسَنْثٜىٰ عَكَيْنَ دَ غِدَنْ بَابَنَ؞ كَيْ سَرْكِے دَ غِدَنْ مُلْكِنْكَ، بَاكُ دَ لَيْڢِے عَثِكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta ce wa sarki, “Ya ubangijina, sarki, bari laifin ya zauna a kaina da gidan mahaifina, sarki kuwa da gadon sarautarsa ya barata.”