2 Samuel 15:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Dawuda ya ce wa dukan fadawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Ku zo! Mu gudu, in ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom. Dole mu bar nan, nan da nan, in ba haka ba zai tashi da sauri yă fāɗa mana, yă kuma hallaka garin da takobi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَثٜىٰ وَمَاسُ يِمَسَ حِدِمَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ تَرٜىٰدَشِ أَ عُرُوشَلِيمَ «كُتَاشِ مُغُدُ! عِدَنْ بَهَكَبَ بَابُوَنْدَ ذَيْ ڟِيرَا دَغَ حَنُّنْ أَبْسَلُوامْ! مُغُدُ دَ سَوْرِ! كَدَ أَبْسَلُوامْ يَسَامٜىٰمُ يَيِ مَنَ ٻَرْنَ يَكَكَّشٜىٰ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنْ دَ تَكُواْبِے!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”