2 Samuel 15:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبْسَلُوامْ يَكَنْ تَاشِ دَ سَسَّڢٜىٰ يَڟَيَ عَكَنْ حَنْيَ ذُوَا ڧُواْڢَرْ غَرِ؞ سَعَدَّ وَنِ يَذُواْ وُثٜىٰوَ وَنْدَ كُمَ يَنَدَ دَامُوَرْ دَ ذَاتَ كَيْ غَبَنْ سَرْكِے دُوانْ شَرِيعَ، أَبْسَلُوامْ يَكَنْ كِرَشِ يَثٜىٰوَ مُتُمِنْ «دَغَ وَنٜىٰ غَرِ كَڢِتُواْ؟» سَعَدَّ مُتُمِنْ يَأَمْسَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ دَغَ غَرِ نَوَتَ ذُرِيَ عَ إِسْرَٰٓءِيلَ،»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da take shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari'a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra'ila,