2 Samuel 15:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zadok yana nan tare da su, kuma dukan Lawiyawan da suke tare da shi kuwa suna ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka sauke akwatin alkawarin Allah, Abiyatar ya miƙa hadaya sai da mutane suka gama fita daga birnin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ظَدُواكْ ڢِرِسْتِ كُوَ يأَنَانً، كُمَ دُكَنْ لَوِيَاوَنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰدَشِ سُنَ طَوْكٜىٰ دَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ نَ اللَّهْ ؞ سُكَ أَجِيٜىٰ عَݣُوتِنْ عَڧَسَا كُسَدَ أَبِيَتَرْ ڢِرِسْتِ، سَيْ دَ مُتَنٜىٰنْ سُكَ ڧَارٜىٰ ڢِتُواْوَ دَغَ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin.