2 Samuel 15:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Absalom kuwa yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Da duk mai ƙara, ko kuka wanda zai zo wurina, zan in tabbatar an yi masa adalci.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبْسَلُوامْ يَكَنْ كُمَ ڧَارَ دَ ثٜىٰوَ «دَاعَثٜىٰ أَنَّطَ نِے مَيْ شَرِيعَ أَوَنَّنْ ڧَسَا دَ كُواْوَنٜىٰ مُتُمِنْ دَ يَكٜىٰدَ ڧَارَ كُواْ مَغَنَرْ شَرِيعَ يَذُواْ وُرِينَ دَ ذَنْ يَنْكٜىٰ مَسَ شَرِيعَرْ غَسْكِيَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakan kuma ƙara da cewa, “Kai, in da a ce ni ne alƙali a ƙasar, zan yi wa duk wanda ya zo wurina da ƙara, shari'ar gaskiya.”