2 Samuel 16:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ دَاوُدَ يَوُثٜىٰ سَمَنْ تُدُنْ كَطَنْ، سَيْ ظِبَ، مَيْ حِدِمَرْ مٜىٰڢِبُواْشٜىٰتْ، يَسَدُ دَشِ؞ ظِبَ يَذُواْ دَ جَاكُنَ بِيُ طَوْكٜىٰ دَ دُنْڧُلٜىٰنْ غُرَاسَ طَرِے بِيُ دَ دُنْڧُلٜىٰنْ بُوسَشّٜىٰنْ إِنَبِے غُدَا طَرِے دَ سَابَبِّنْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰ غُدَا طَرِے دَ سَلْكَرْ ضُوً إِنَبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin 'ya'yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi.