2 Samuel 16:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَهِتُواْڢٜىٰلْ يَثٜىٰ مَسَ «كَتَڢِے كَݣُونَ دَ مَاتَانْدَ بَابَنْكَ يَبَرِ دُواْمِنْ سُلُورَ دَ غِدَنْ سَرْكِے؞ تَهَكَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاسُجِ ثٜىٰوَ كَثِ مُتُنْثِنْ بَابَنْكَ؞ وَنَّنْ ذَيْ ڧَارَ ڧَرْڢَڢَ دُكَنْ مَاسُ غُواْيُوانْ بَايَنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra'ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.”