2 Samuel 17:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ مُتَنٜىٰنْ أَبْسَلُوامْ سُكَ تَڢِے، سَيْ أَهِمَعَظْ دَ يُواْنَتَنْ سُكَ ڢِتَ دَغَ رِجِيَرْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ سَرْكِے دَاوُدَ سُكَثٜىٰ مَسَ «يِمَظَا كَڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ! غَمَا غَا إِرِنْ شَوَرَرْ دَ أَهِتُواْڢٜىٰلْ يَبَايَرْ عَكَنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.”