2 Samuel 17:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبْسَلُوامْ كُوَ يَسَا أَمَسَ يَذَمَ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ أَمَيْمَكُوانْ يُواْوَبْ؞ أَمَسَ طَنْ عِتَرَ نٜىٰ، وَنِ مُتُمِنْ ذُرِيَرْ إِسْمَٰعِيلُ؞ عِتَرَ يَ عَوْرِ أَبِغِيٜىٰلْ یَرْ نَهَشْ، وَدَّ تَكٜىٰ یَرْعُوَرْ ظٜىٰرُوِيَ، وَتُواْ مَامَرْ يُواْوَبْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab.