2 Samuel 17:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَڧِيلَ يَنْذُ يَٻُيَ أَوَنِ كُواْغُواْ كُواْ كُوَ وَنِ وُرِے؞ عِدَنْ كُوَ عَيَاڧِ نَڢَارِ، كَطَنْ دَغَ ثِكِنْ سُواْجُواْجِنْكَ سُكَ مُتُ، دُكْ وَنْدَ يَجِ لَابَرِ ذَيْثٜىٰ، ‹أَنْ كَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ أَبْسَلُوامْ دَيَوَ!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu haka yana cikin rami ko dai a wani wuri a ɓoye. Idan an kashe waɗansu daga cikin mutanenka a karo na farko, duk wanda ya ji zai ce, ‘An kashe mutane da yawa daga cikin mutanen Absalom.’