2 Samuel 18:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سُواْجَنْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «بَذَنْ تَٻَ طَنْ سَرْكِے بَ، كُواْ دَمَا كَبَانِ أَظُرْڢَا دُبُو أَ هَنُّونَ؞ غَمَا دُكَنْمُ مُنْجِ سَعَدَّ سَرْكِے يَكٜىٰ بَاكُ عُمَرْنِ، كَيْ دَ أَبِشَيْ دَ كُمَ إِتَّيْ ثٜىٰوَ ‹سَبُواْدَنِ كُكِيَايٜىٰ مِنِ سَوْرَيِنَّنْ أَبْسَلُوامْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, ‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.’