2 Samuel 18:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَرَبَسُ كَشِ عُكُ؞ يُواْوَبْ يَشُوغَبَنْثِ كَشِ نَطَيَ، أَبِشَيْ طَنْعُوَنْ يُواْوَبْ طَنْ ظٜىٰرُوِيَ يَشُوغَبَنْثِ كَشِ نَبِيُ؞ سَيْ كُمَ إِتَّيْ مُتُمِنْ غَتْ يَشُوغَبَنْثِ كَشِ نَعُكُ؞ سَعَنً دَاوُدَ يَثٜىٰ مُسُ «نِے دَكَيْنَ ذَنْبِيكُ ذُوَا يَاڧِنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”