2 Samuel 18:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ahimawaz ya tā da murya ya ce wa sarki, “Kome lafiya yake!” Sai ya rusuna har ƙasa a gaban sarki ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka! Ya ba da mutanen da suka tayar wa ranka yă daɗe a hannunsa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَهِمَعَظْ يَطَغَ مُرْيَ يَثٜىٰ وَ سَرْكِے «كُواْمٜىٰ يَنَ لَاڢِيَ!» سَيْ يَرُسُنَ دَ ڢُسْكَرْسَ حَرْ ڧَسَا يَثٜىٰ «أَلْبَرْكَ تَا تَبَّتَا غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكَ، وَنْدَ يَكُٻُتَرْ دَكَيْ دَغَ حَنُّنْ مَاسُ غَابَادَ سَرْكِے، رَنْكَيَدَطٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”