2 Samuel 18:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya ce, “Saurayin nan Absalom yana nan da rai?” Ahimawaz ya ce, “Na ga wani babban rikicewar a daidai lokacin da Yowab yake gab da aikan bawan sarki da kuma ni, sai dai ban san ko mene ne ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «سَوْرَيِنَّنْ أَبْسَلُوامْ يأَنَانً لَاڢِيَ؟» أَهِمَعَظْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، أَ سَعَدَّ يُواْوَبْ يَعَيْكٜىٰنِ، نَغَ بَبَّنْ تَاشِنْ حَنْكَلِ عَمَّا بَنْ سَنْ كُواْ مٜىٰنٜىٰنٜىٰبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?” Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”