2 Samuel 18:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma mutanen suka ce, “Ba za ka fita ba; gama in ya kasance tilas mu gudu, ba za su kula da mu ba. Ko da rabinmu sun mutu, ba za su damu ba; amma kai kanka ka fi mutum dubu goma namu. Zai fi maka ka zauna a cikin gari, ka dinga aika mana da taimako.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ أَمْسَ مَسَ سُكَثٜىٰ «أَعَ، بَذَاكَ بِيمُبَ! غَمَا كُواْ دَمُنْ غُدُ عَيَاڧِنْ، مُتَنٜىٰنْ أَبْسَلُوامْ بَذَاسُ دَامُبَ؞ كُواْ دَمَا رَبِنْمُ سُنْ مُتُ، بَذَاسُ دَامُبَ؞ غَمَا كَيْنٜىٰ سُكٜىٰ نٜىٰمَ، غَمَا كَا ڢِے مُسُ مُتُمْ دُبُو غُواْمَ نَمُتَنٜىٰنْمُ؞ ذَيْڢِے ݣَوْ كَذَوْنَ عَبِرْنِ كَعَيْكَ مَنَ دَ تَيْمَكُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”