2 Samuel 18:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya ce, “Zan yi duk abin da ya fi muku kyau.” Saboda haka sarki ya tsaya kusa da bakin ƙofa yayinda dukan mutane suke fitowa a ƙungiyar ɗari-ɗari da ta dubu-dubu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَأَمْسَ يَثٜىٰ «تُواْ، ذَنْيِ أَبِنْدَ كُكَغَ يَدَاثٜىٰ؞» سَيْ يَڟَيَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ بِرْنِنْ يَايِنْ دَ سُواْجُواْجِنْ سُكٜىٰ وُثٜىٰوَ ڧُنْ‌غِيَ طَرِے طَرِے دَ ڧُنْ‌غِيَ دُبُو دُبُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.