2 Samuel 19:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Sarki Dawuda ya aika da saƙo zuwa wurin Zadok da Abiyatar, firistoci, ya ce, “Ku tambayi dattawan Yahuda, ‘Me ya sa ku ne za ku zama na ƙarshe a yin tunanin komar da sarki zuwa fada, da yake abin da ake faɗi ko’ina a Isra’ila ya kai kunnen sarki a mazauninsa?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَرْكِے دَاوُدَ يَجِ لَابَرِنْ أَبِنْدَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكٜىٰثٜىٰوَ سَيْ يَعَيْكَ دَ سَڧُواْ وُرِنْ ظَدُواكْ دَ أَبِيَتَرْ ڢِرِسْتُواْثِے؞ يَثٜىٰمُسُ «كُتَمْبَيِ دَتَّاوَنْ يَهُودَ كُثٜىٰ مُسُ، ‹دُوانْمٜىٰ كُونٜىٰ نَڧَرْشٜىٰ ثِكِنْ مَاسُ نٜىٰمَنْ دَاوُاْ دَ سَرْكِے غِدَنْسَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da labarin abin da Isra'ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa.