2 Samuel 19:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَكَامَ حَنْيَ ذَيْ كُواْمَ عُرُوشَلِيمَ؞ يَكَيْ بَاكِنْ كُواْغِنْ يُواْدَنْ كٜىٰنَنْ، سَيْ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَذُواْ غِلْغَلْ دُواْمِنْ سُتَرْيٜىٰشِ سُكُمَ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ دَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun.