2 Samuel 19:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da ’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِمٜىٰيِ يَذُواْ تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ بِلِيَامِنُ غُدَا دُبُو؞ ظِبَ مَيْ حِدِمَرْ غِدَنْ طَالُوتَ شِے مَا يَذُواْ تَرٜىٰدَ یَیَنْسَ مَظَا غُدَا غُواْمَشَا بِيَرْ دَ بَايِنْسَ غُدَا عَشِرِنْ؞ دُكْ سُكَ تَڢِے دَ سَوْرِ سُكَ غَنْغَرَ ذُوَا بَاكِنْ كُواْغِنْ يُواْدَنْ دُواْمِنْ سُسَدُ دَ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya zo tare da mutum dubu (1,000) daga kabilar Biliyaminu. Ziba kuma, baran gidan Saul, ya zo a gaggauce a gaban sarki a Urdun tare da 'ya'yansa maza, su goma sha biyar, da barorinsa guda ashirin.