2 Samuel 19:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka haye a mashigin don su ƙetaro da iyalin sarki, su kuma yi duk abin da yake so. Sa’ad da Shimeyi ɗan Gera ya haye Urdun, sai ya fāɗi rubda ciki a gaban sarki
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ دُواْمِنْ سُهَيٜىٰ دَ سَرْكِے دَ مُتَنٜىٰنْسَ، سُكُمَيِ أَبِنْدَ يَكٜىٰسُواْ؞ سَعَدَّ سَرْكِے يَكٜىٰ شِرِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ، سَيْ شِمٜىٰيِ يَذُواْ يَڢَاطِ أَغَبَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi. Sa'ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa.