2 Samuel 19:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دَاوُدَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «وَنٜىٰنٜىٰ يَتَمْبَيِ رَعَيِنْكُ، كُو یَیَنْ ظٜىٰرُوِيَ؟ كُنَسُواْ كُجَٰوُاْ مِنِ وَهَلَ نٜىٰ؟ يَنْذُ نَا سَنِ نِنٜىٰ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كُمَ بَابُ مُتُمِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَنْدَ ذَاعَ كَشٜىٰ يَوْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.”