2 Samuel 19:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مٜىٰڢِبُواْشٜىٰتْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، كَا سَنْ نِے غُرْغُنٜىٰ؞ أَسَعَدَّ نَثٜىٰ وَ ظِبَ مَيْيِ مِنِ حِدِمَ يَشِرْيَ مِنِ جَاكِ إِنْهَوْ إِنْبِے سَرْكِے، سَيْ يَرُوطٜىٰنِ يَتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mefiboshet ya amsa ya ce, “Ya ubangijina, sarki, barana ya ruɗe ni, gama na ce masa ya yi wa jaki shimfiɗa don in hau in tafi wurin sarki, gama ka sani ni gurgu ne, ranka ya daɗe.